Ƙarƙashin yarjejeniyar da ake fatan ƙullawa don kawo ƙarshen yaƙin na watanni 11 tsakanin Isra’ila da Hamas, matakin Netanyahu na ganin lallai sai ƙasar shi ta karɓe ragamar yankin Salahadden ko kuma Philadelphi na cikin jerin sharuɗɗan da Hamas ta ƙi aminta da su, la’akari da yadda yankin ke matsayin iyakar kudancin Gaza da Masar.
Sai dai Firaminista Netanyahu ya ce har sai Isra’ila ta karɓe iko da yankin na Salahadden ne za ta iya rusa Hamas, bayan da ta yi zargin cewa ta wannan iyakar ne ake shigarwa da ƙungiyar makamai.
A ɓangare guda Hamas ta yi watsi da duk wani yunƙurin ci gaba da kasancewar Sojin Isra’ila a yankin bare akai ga batun ƙwace iko da wannan iyaka mai matuƙar muhimmanci ga Gaza.
Tuni dai zanga-zanga ta tsananta a sassan Isra’ila tare da buƙatar lallai Firaminista Netanyahu ya sanya hannu kan yarjejeniyar cikin gaggawa don tseratar da sauran fursunonin da ke hannun Hamas.
Ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant a wani jawabinsa gaban manema labarai, ya ce wannan mataki na Netanyahu ya harzuƙa ƙasashe da dama ciki har da manyan ƙawayen Isra’ila irin Amurka, batun da ministan ke cewa akwai buƙatar janyewar dakarun nasu kamar yadda Hamas ta buƙata.
Akwai dai zargin kasancewar tarin ramukan ƙarƙashin ƙasa daga iyakar ta Philadelphi wadda ake amfani da ita wajen safarar haramtattun kayaki zuwa cikin Gaza ba tare da sanin Isra’ila wadda ke ci gaba da mamaya ga ilahirin yankin na Falasɗinu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI