Zanga-Zanga game da Yaman a Ingila

A Landan Babban Birnin Ingila an gudanar da zanga-zangar adawa ga kasashen Tarayyar Turai da Ingila da ke sayarwa da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa makamai inda suke kai hare-hare a Yaman.

Masu zanga-zangar sun taru a gaban ofishin BBC tare da yin tattaki zuwa gaban Fadar Firaminista.

Masu zanga-zangar dauke da tutar Yaman sun dinga daga allunan da aka rubuta "Ku dakatar da kai hare-hare", "Adalci ga Yaman", "Ku kubutar da Yaman", "Ku kauracewa Hadaddiyar Daular Larabawa" da "Ku dakatar da Saudiyya".

A jawaban da aka yi a wajen zanga-zangar an bayyana cewar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa na kai hare-hare da makaman da suka saya daga kasashen Tarayyar Turai da Ingila, a saboda haka aka bukaci da su dakatar da sayar musu.

Masu zanga-zangar sun kuma hadu da masu zanga-zangtar adawa da nuna wariya a kusa da ginin majalisar dokokin Ingila. Masu adawa da nuna wariyar5 sun bayar da taimako ga gangamin taimakawa Yaman da ake yi.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewar mutane kusan dubu 230 ne suka mutu a Yaman sakamakon yaki, kwalara, karancin abinci da annoba da ke damun kasar.


News Source:   www.trt.net.tr