Masanan sun ce ko da an faro aikin kwashe wannan ɓaraguzan gine-gine a yanzu, zai ɗauki aƙalla shekaru 10 gabanin nasarar kwammale yashe shi daga tsakar Gaza.
A cewar alƙaluman da masana gine-ginen suka tattara, ana buƙatar aƙalla dala miliyan 700 gabanin iya gudanar da aikin kwashe wannan ɓaraguzai a wani yanayi da yanzu haka Falasɗinawa miliyan 1 da dubu 900 ke rayuwa babu matsuguni.
Bayanai sun ce hatta a yankunan da Falasɗinawa suka fice tun a farko fara yaƙin Sojin Isra’ila sun ci gaba da jefa bama-bama kan gidajen jama’a tare da rushe su, yayinda a wasu yankunan aka ga yadda motocin rusau suka shiga tare da niƙe dubunnan gine-gine.
Wannan gine-gine a cewar alƙaluman da kafar AlJazeera ta tattara sun ƙunshi asibitoci da makarantu da hukumomi da ma’aikatun gwamnatin yankin na Gaza baya ga gidajen ɗaiɗaikun jama’a.
Yanzu haka mutane sun fara komawa gidajensu musamman waɗanda suka fito daga yankin arewacin Gaza sai dai ga dukkan alamu gidajen baza su zaunu ba lura da yadda galibinsu suka koma kufai.
Tsawon watanni 15 Isra'ila ta shafe ta na luguden wuta kan al'ummar yankin na Gaza tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da Hamas ta kai mata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI