Zaftarewar kasa a Indonesiya

Zaftarewar kasa a Indonesiya

Mutane 10 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 9 suka bata sakamakon zaftarewar kasa da ta afku sanadiyyar mamakon ruwan sama jiya da yamma a yankin Nganjuk na lardin Gabashin Java da ke kasar Indonesiya.

An samu mummunar barna a cikin gidaje 8 sakamakon zaftarewar ƙasar a ƙauyen Ngetos.

Adadin mutanen da suka bata, wanda a baya aka sanar da cewa sun kai 20 yanzu sun kasance 21. Adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 10 bayan da aka gano gawarwakin wasu karin mutane 8 a kokarin aikin bincike da ceto da ake gudanarwa.

Har zuwa yanzu ana ci gaba da neman mutane 9 da suka bata a yankin da zaftarewar kasar ta afku inda aka gano mutane 2 da rai a karkashin kasa.

A halin da ake ciki, an kwashe mutane 147 wadanda bala’in ya shafa da wasu 16 da suka jikkata zuwa wasu yankunan.

Ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa na yawan afkuwa a Indonesiya a yankin Equator, musamman a lokacin Oktoba zuwa Afrilu.


News Source:   ()