An sanar da rasa rayuwar wani dan yawon bude ido sakamakon zubar dusar kankara a kasar Kazakistan.
An sanar da cewa a yayinda wasu 'yan yawon bude ido su 6 ke rangadi akan babura a birnin Ridder dake Gabashin Kazkistan dusar kankarar ya zaftane.
Kamar yadda Ma'aikatar Bayar Da Agajin Gaggawan kasar Kazakistan ta sanar mutum daya ya rasa ransa yayinda aka kubutar da wasu biyar da dusar kankarar ta taushe.
An bayyana cewa wanda ya rasa rayuwarsa an haifeshi a shekarar 1979.
Hukumomin yankin sun fadakar da a dauki matakai tsantsan a yayinda ake ziyartar yankin. An kuma yi kira da kada a ziyarci yankin da dusar kankarar ke zuba.