An sanar da cewa afkuwar zabtarewar kasa a jihar Gazne dake kasar Afghanistan ta yi sanadiyar rayukan mutum uku.
Mai magana da walin Gazne,Wahidullah Cumazadeh, ya shaidawa manema labarai da cewa a kauyen Gaygantu dake karkashin gundumar Malistan a jihar Gazne zabtarewar kasa ta afku tare da hallaka mutum uku.
Cumazadeh, ya kara da cewa bala'in ta yi kuma sanadiyar rushewar gidaje da dama.