Za’a zauna karo na hudu akan samar da kudin tsarin mulkin Siriya

Za’a zauna karo na hudu akan samar da kudin tsarin mulkin Siriya

An sanar da cewa za a fara zaman samar da kundun tsarin mulkin Siriya karo na hudu a ranar Litini a birnin Geneva akan samar da dokokin da zasu samawa kasar zaman lafiya mai dorewa.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musanman a Siriya ya shaidawa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da cewa an kammala shirin zama karo na hudu akan samar da kundin tsarin mülkin Siriya.

Kwamitin za ta zaune ne tsakanin 30 ga watan Nuwamba zuwa 4 ga watan Disamba kamar yadda mai magana da yawun ofishin samar da kundin tsarin mulkin Jennifer Fenton ta shaidawa kanfanin dillancin labaran Anadolu.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musanman a Siriya Geir Pedersen ne zai jagoranci zaman samar da tsarin mulkin Siriya karo na hudu wanda za’a kammala a ranar 4 ga watan Disamba.


News Source:   ()