Za’a bunkasa hadin gwiwa tsakanin sojojin Turkiyya da Amurka

Za’a bunkasa hadin gwiwa tsakanin sojojin Turkiyya da Amurka

Ministan harkokin tsaron kasar Turkiyya Hulusi Akar ya tattauana da takwaransa na Amurka Lloyd Austin akan tsaron yanki da kuma yunkurin bunkasa tsaro tsakanin kasashen biyu.

Ministan tsaron Turkiyya Hulusi Akar da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin sun yi musayar bayanai akan muhinmancin aikin kasashen biyu tare domin inganta tsaro.

Sun yi nuni ga muhinmancin ci gaba da aiki tare da kuma yin musayar bayanai akan bunkasa tsaro a doron kasa da kuma a yankin.

Ma’aikatar tsaron kasar Turkiyya da ta fitar da sanarwar ta kara da cewa Akar da Austin sun jaddada bayar da hadin kai yadda zasu yi aiki tare da kuma bunkasa huldan sojin kasashen biyu.


News Source:   ()