Za mu miƙa wa Donald Trump mulki cikin lumana - Biden

Za mu miƙa wa Donald Trump mulki cikin lumana - Biden

Shugaba Joe Biden ya yi wannan alkawarin ne yayin jawabinsa na farko ga Amurkawa bayan zaɓen ranar 5 ga watan Janairu, inda tsohon shugaban ƙasar Donald Trump ya doke mataimakiyar shugaban ƙasa Khamala Haris da gagarumin rinjaye.

Shugaban Biden cikin murmushi ya yi alkawarin tabbatar mika mulki cikin lumana a ranar 20 ga watan Janairu lokacin da za a rantsar da tsohon shugaban ƙasa kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Donald Trump a matsayin shugaban Amurka na 47.

"Zan yi aikina a matsayina na shugaban kasa”, kamar yadda Biden ya shaidawa taron manyan jami'ai da ma'aikata yayin wani taƙaitaccen jawabi na mintuna bakwai ranar Alhamis a Lambun Rose na Fadar White House.

Da yake mika sakon taya murna ga Trump, Biden ya ce sun amince da zaɓin yan ƙasa.

Biden ya kuma jinjinawa mataimakiyarsa Kamala Harris bayan tattaunawa da ita ta wayar tarho, yana mai yabawa nasarori da ta samu a yaƙin neman zaɓe mai cike da armushi duk da ba ta yi nasara ba a zaɓen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)