Ayatollah ya faɗi haka ne a yayin gabatar da huɗubar juma’a ta farko cikin shekaru masu yawa.
Ku latsa hoton bidiyon da ke kasa domin kallon jawabinsa da ya yi wa dandazon Iraniyawa a wannan Juma'ar.
Jawabin Ayatollah ga Iraniyawa 01:38Domin nuna wannan labarin, akwai bukatar ka bayar da izinin sanin bayanan masu bibiya da tallace-tallacen kundin adana bayanai na cookies
Amince Zabin son raina Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei. AP - Vahid SalemiMayar da hankalin da Amurka ta yi da kawayenta kan bai wa Isra’ila kariya, ba don komai ba ne, illa don ta ci gaba da kwashe albarkatun ƙarƙashin ƙasar yankin gabas ta tsakiya tare da zuba arzikin cikin haddasa yaƙi a duniya. Burinsu shi ne su mayar da Isra’ila a matsayin wwata kofar fitar da makamashi daga yankin zuwa ƙasashen yammacin duniya, sannan kuma su rika shigo da kayayyaki cikin yankin ta kofar Isra’ila- Inji Ayatollah
Jagoran ya kara da cewa, "A lokacin da muguwa kuma matsoraciyar abokiyar gaba ta gaza samun cikakkiyar nasarar tarwatsa ƙarfin Hezbollah da Hamas ko Islamic Jihad da sauran ƙungiyoyi, sai ta fara iƙirarin nasara ta hanyar kisan giulla da lalata gine-ine da kuma kai hari tare da kashe fararen hula."
Jagoran ya kuma buƙaci Iraniyawa da ruɓanya ƙoƙarinsu da ƙarfinsu, da kuma haɗa kansu tare da turjiya ga Isra'ila da ya bayyana a matsayin muguwar abokiyar gaba.
Kazalika Ayatollah ya buƙaci ƙasashen Larabawa da su haɗa kansu domin tunkarar barazanar da yankin Gabas ta Tsakiya ke fuskanta a wannan lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI