Za mu dakatar da farmaki muddin Rasha ta amince da zaman lafiya - Ukraine

Za mu dakatar da farmaki muddin Rasha ta amince da zaman lafiya - Ukraine

Wannan na zuwa ne bayan sojojin Ukraine sun kutsa cikin yankin Kursk mallakin Rasha a Talatar makon jiya, inda suka ƙarɓe iko da wurare da dama  a ƙarkashin farmaki mafi girma da wata rundunar soji daga ƙetare ta kai cikin kwaryar Rasha tun bayan yaƙin duniya na biyu.

Tuni sama da mutane dubu 12 suka arce daga yankin, yayin da shugaban rundunar sojin Ukraine, Oleksandr Syrsky ya ce, dakarun nasa na rike da yankin da faɗinsa ya kai murabba’in kilomita dubu 1,000 a Rasha.

Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Ukraine ta ce, ko kaɗan, Kyiv ba ta da aniyar mallake wani yanki na Rasha, amma ta ce, abin da sojojin suka yi bai saɓa wa doka ba.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Ukraine ɗin ta ce, da zaran Rasha ta amince da tayin zaman lafiya kaɗai, to babu shakka sojojin za su fice daga wannan yanki da suka mamaye tare da dakatar da farmakin da suke ƙaddamarwa.

A ɓangare guda, Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta ce, ta yi nasarar daƙile sabbin hare-haren da Ukraine ta ƙaddamar a Kursk.

A cikin watan Fabairun 2022 ne Rasha ta fara luguden wuta kan Ukraine, kuma ta yi nasarar mamaye wasu wurare a cikin ƙasar makwabciyarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)