Za'a hangi Mars daga duniya a cikin wannan watan

Masana ilimin sararin samaniyya sun sanar da cewa duniyar Mars za ta kusanci duniya a cikin watan  da muke ciki na Oktoba.

Hukumar nazarin sararin samaniyya ta kasar Amurka watau NASA ce ta sanar da cewa duniyar Mars za ta kasance kusa da duniyarmu yadda za'a ma iya hangenta a cikin watan Oktoba.

NASA ta kara da cewa ana samun hakan sau daya a cikin ko wane shekaru 15, inda ta kara da cewa a wannan karon a cikin watan da mmuke ciki ne Mars zata kusance duniyarmu.

Hukumar NASA ta jaddada cewa a ko wace yamma mars zata haskaka gabashi da kuma yammaci kafin wayewar gari.

A ranar 6 ga watan Oktoba dai ne Mars ta fi kusantar duniyar wanda ba'a taba ganin hakan ba tun bayan shekarar 2003.

Mars zata sake kusantar duniya ne kuma a shekarar 2035.

 


News Source:   ()