Firaiministan Kazakistan Askar Mamin ya bayyana cewa za a gina layin dogo tsakanin Kazakistan zuwa Turkmenistan.
A taron kwamitin ministocin da shugaban kasar Kazakistan Kasim Comert Tokayev ya jagoranta ne firaiministan kasar Askar Mamin ya bayyana cewa za a saka hannun jari a fannonin sufuri da yawun bude ido na dala bilioyan 2.6 a kasar.
Ya kara da cewa musanman a fannin yawon bude ido kasar za ta mayar da himma inda za ta gina layin dogo daga zuwa kasar Turkmenistan.
Mamin ya kara da cewa layin dogon da zai kai har babbban birnin Tashkent zai kuma hade biranen Turkistan-Chimken-Tashkent.