Masana kimiyya da fasaha a kasar Holan sun fara horar da ƙudan zuma don gano sabbin nau'ikan kwayar cuta (Kovid-19).
Masana kimiyya a Jami'ar Wageningen sun yi amfani da shahararriyar hanyar gwajin wacce aka fi sani da Karen Pavlov don horar da kudan zuma.
A cikin horon, an kan baiwa kudan zuma ruwan suga idan ya iya gano kwayar cutar ta korona.
Ba a baiwa kudan zuman lada a lokacin da bai gano kwayar cutar ba.
Masana kimiyya sun bayyana cewa ƙudan zuma na iya gano ƙwayoyin cuta a cikin sakan, wanda hakan zai rage lokutan jira na hanyoyin da ake amfani dasu a halin yanzu.