Shugaban Hukumar Tarayyar Musulmi a Kudus ya sanar da cewa za'a bude Masallacin Masjid Al-Aksa dake gabashin Kudus inda Isra'ila ke mamaya bayan bukukuwan karamar sallah.
Hukumar dake da hadaka da Kungiyoyi masu zaman kansu a Jordan, Masu yiwa Islma hidima da Hukumar Mukaddesat ta sanar da cewa Masallacin da aka rufe a watan Maris sanadiyar bulluwar kwayar cutar Covid-19 za'a bude shi bayan salla sabili da nasarorin da aka samu na yaki da cutar.
An dai rufe Masjid Al-Aksa baki daya tun daga ranar 22 ga watan Maris sanadiyar cutar da Corona.
Hukumar ta tunatar da cewa domin kara daukar matakan yakar sabuwar kwayar cutar corona Masjid Al-Aksa ya kasance a rufe a cikin watan Ramadana.