
A lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen wani taron manema labarai gabanin buɗe taron na kwanaki biyu kan fasahar ta AI, Macron da firaministan India Narendra Modi, sun ce taron na da ƙudirin cimma manufofin shata algiblar gudanar da fasahar AI a duniya, da bai wa jama’a damar bayyana ra’ayinsu kan fasahar da kuma matsayar Turai kan ta.
Gabanin fara taron dai, ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da wasu kamfanonin Faransa, sun sanar da aniyarsu ta zuba jarin euro biliyan 109, ciki har da gina cibiyar tattara bayanai kan fasahar ta AI a Faransa.
Taron da za a fara a yau litinin wanda zai samu halartar kusan baƙi mutum dubu 1 da ɗari 5, masana za su gabatar da laccoci da tattaunawa kan ci gaba da ƙalubalen da fasahar ke fuskanta.
Haka nan, shugaba Macron na son ya yi amfani da damar taron, don nuna irin ci gaban da ɓangaren fasahar Faransa ya samu, wanda a yanzu haka ke da kusan kamfanoni 750 da ke aiki a fannin fasahar AI.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI