Za a yankewa zaɓaɓɓen shugaban Amurka hukunci akan wasu tuhume-tuhume

Za a yankewa zaɓaɓɓen shugaban Amurka hukunci akan wasu tuhume-tuhume

Hukuncin mai shari’a Juan Merchan na nufin cewa za a bukaci Trump ya bayyana a gaban kotu kwanaki 10  kafin rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairu, lamarin da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin Amurka.

Kafin Trump, babu wani shugaban Amurka tsoho ko na kan karagar mulki da aka taɓa tuhumarsa da aikata wani laifi ko kuma aka same shi da laifi.

Hukuncin dai zai baiwa Trump damar daukaka ƙara indai ya buƙaci yin hakan a duk lokacin da ya ga dacewar hakan.

Merchan ya amince a hukuncin da ya yanke cewa Trump, ya bayyana cewa yana da niyyar daukaka kara.

A wani sako da ya wallafa a kafar sadarwarsa ta yanar gizo a safiyar ranar Asabar, Trump ya ce bai taba ƙumbiya-ƙumbiya a bayanan kasuwanci ba a dukkanin harkokinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)