An sanar da cewa jiragen sama tsakanin birnin Sulaimaniyah da ke Iraki da Turkiyya za su ci gaba a ranar 26 ga watan Oktoba.
A cikin rubutacciyar sanarwar da Filin Tashi da Saukar Jiragen Sama na Sulaymaniyah ya fitar, za a fara zirga-zirgar jiragen sama da Turkiyya a ranar 26 ga Oktoba.
A sanarwar an bayyana cewar za a fara zirga-zirgar jirage biyu na mako-mako tsakanin Turkiyya da birnin Sulaimaniyah.
A wata rubutacciyar sanarwa da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Iraki ta fitar a ranar 15 ga watan Oktoba, an sanar da sake fara zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Iraki da Turkiyya wanda aka dakatar a farkon wannan watan.
A sanarwar an bayyana cewar za a yi zirga-zirgar jiragen sama 7 a kowane mako tsakanin kasashen biyu.
A ranar 1 ga Oktoba aka dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Turkiyya da Iraki.
Babu wani bayani da Iraki ta bayar game da dalilin dakatar da zirga-zirgar jiragen.