Za a gwada allurar BCG don ganin ko za ta iya zama riga-kafin cutar Corona

Za a gwada allurar BCG (Riga-kafin tarin fuka) don ganin ko za ta iya zama riga-kafin cutar Corona (Covid-19) ko kuwa a'a.

Tashar BBC ta bayyana cewar, a karkashin wasu aiyukan bincike na kasa da kasa, an fara gwada allurar BCG da aka samar a shekara 1921 don bayar da riga-kafi ga tarin fuka da sauran wasu cututtuka masu yaduwa, don ganin ko za ta iya zama riga-kafin cutar Corona.

An fara gwajin a kasashen Ingila, Ostireliya, Holan, Spaniya da Barazil.

A aiyukan da aka fara karkashin jagorancin Jami'ar Exeter da ke Ingila, za a yi wa mutane dubu daya allurar BCG, sannan a sanya idanu kan ko za su kamu da cutar Corona ko kuma ba za ta kama su ba.

An bayyana cewar za a gwada mafi yawan allurar kan ma'aikatan lafiya da su ne suka fi fuskantar hatsarin kamuwa da cutar.

Daga cikin marubutan wata makala da mujallar Lancet ta wallafa akwai Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) Dr. Tedros Adhanov Ghebreyesus wanda bayyana cewar, allurar BCG na da ikon zama riga-kafin Corona har zuwa lokacin da za a samar da cikakken riga-kafin cutar.


News Source:   ()