Za a gudanar da Babban Taron Kwamitin Dabaru na Turkiyya da Katar Karo na 6 tare da halartar Shugaba Recep Tayyip Erdogan da Shugaban Katar Sheikh Tamim bin Hamad Al Sani gobe a Ankara, babban birnin kasar Turkiyya.
A rubutacciyar sanarwar da Ma’aikatar Sadarwa ta Shugaban kasa ta fitar an bayyana cewar za a gudanar da taron da mai martaba Sarkin Katar Al Sani zai jagoranta a Turkiyya, za a sake duba dukkan bangarorin alakar da ke tsakanin Turkiyya da Katar.
A yayin taron, za a tattauna matakan da za a iya dauka don kara zurfafa hadin gwiwar da aka bunkasa bisa tushen kawance, za a yi musayar ra'ayoyi kan ci gaban yankin da na duniya da kuma huldar da ke tsakanin kasashen biyu.
Ana sa ran sanya hannu kan yarjejeniyoyin da zasu taimaka wajen alakar da ke tsakanin kasashen biyu yayin taron kwamitin.