Za a fara sauraron ƙarar kamfanin hada-hadar kuɗin internet na Binance mako mai zuwa a Najeriya

Mai shigar da ƙara ya ce hakan ya biyo bayan buƙatar da lauyan waɗanda ake ƙara ya shigar yana neman sauyin lokacin sauraronta.

Kamfanin Binance da shugaban sashen lura da laifukan dake da alaƙa da kuɗi ɗan asalin ƙasar Amurka, Tigan Gambaryan da manajan kamfanin mai kula da nahiyar Afirka ɗan asalin ƙasar Kenya, Nadeem Anjarwalla dukkaninsu ana zarginsu da safarar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba da yawansu ya kai dala miliyan 35.

Binance ne kamfani mafi girma a hada-hadar kudin internet a duniya kuma ana zarginshi da taka ka’idojin haraji a Najeriya. Sai dai dukkanin waɗanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake tuhumarsu da shi a kotun.

Tuni guda daga shugabannin kamfanin da aka tsare Ajarwallah ya tsere daga hannun jami’an tsaron ƙasar tun kafin fara shari’ar.

Ana tsare da Gambaryan a Najeriya tun watan Fabarairu kuma matarshi mai suna Yuki ta nuna damuwa kan lafiyar mijinta. Ta buƙaci hukumomin Najeriya su saki mai gidan nata saboda halin da lafiyarshi ke ciki, ta kuma buƙaci hukumomin Amurka su taimaka domin ganin an sakeshi.

Gwamnatin Najerya dai ta zargi kamfanin Binance da hannu wurin gurgunta tattalin arziƙin ƙasar bayan da shafinsu ya zama wata matattara da ake hada-hadar Naira da Dalar Amurka inda hakan ya haddasa ƙarancin Dala da ma faɗuwar Naira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)