Kamfanin samar da magunguna na Jamus CureVac ya samu izinin gwada allurar riga-kafin cutar Corona (Covid-19) a kan mutane.
Sanarwar da aka fitar daga kamfanin CureVac ta ce a Jamus da cibiyar Paul Ehrlich ta bayar da damar a yin bincike kan allurar riga-kafin da Hukumar Kula da Magunguna ta Tarayya ta Beljiyom sun amince da su yi amfani da mutane wajen gwajin allurar riga-kafin Corona mRNA da suka samar.
CureVac ya shaida cewar baya ga kamfanin BioNTech da likitan Turkiyya ya mallaki wani bangaren sa, su ne kamfani na 2 da aka ba wa izinin gwajin allurar riga-kafin cutar ta Corona.
Mahukuntan kamfanin sun ce za a magungunan a kasashen Jamus da Beljiyom, kuma nan da tsakiyar shekara mai zuwa magungunan za su fita kasuwa.