Bayan shekaru 18 gwamnatin Iraki ta sake dawo da dokar wajabcin aikin soji inda aka aikewa majalisar dokoki don amincewa da dokar.
Sanarwar da aka fitar daga Ofishin Firaministan Iraki ta ce, a yayin zaman majalisar zartarwa na wannan makon ne aka tattauna game da dokar, kuma Ministoci sun amince da ita inda aka aika ta zuwa majalisar dokoki.
A 'yan kwanaki masu zuwa ake sa ran majalisar dokokin Iraki za ta yi muhawara game da dokar.
A shekarar 2003 bayan Amurka ta mamayi Iraki aka janye dokar wajabcin yin aikin soji ga maza.