A yayin da cutar ta COVID-19 ta addabi bangaren yawon shakatawa, ayyukan otal-otal, gidajen abinci da sauran abubuwan samun kuɗi, birai masu jin yunwa a tsibirin shakatawa na Bali suma sun rasa babban tushen abincin su, lamarin da ya sanya sun kai farmaki gidajen mazauna kauyukan yankin domin neman abinda zasu ci.
Mazauna kauyen Sangeh sun ce birai nau'ukan macaques masu launin toka suna ta fita daga wani wuri mai nisan mita 500 (kusan ƙafa 1,600) don yin liyafa a kan rufinsu kuma suna jiran lokacin da ya dace don sauka da kwace abin ci.
Sun damu matuka cewa ire-iren wadannan hare-haren za su kai ga hare-haren birai a kan ƙauyen, mazauna garin suna ɗaukar 'ya'yan itace, gyada da sauran abinci zuwa dajin Sangeh inda biran suke don ciyar dasu.
Saskara Gustu Alit, wani mazauni kauyen ya ce "Muna tsoron kada birrai masu jin yunwa su rikide zuwa namun daji masu cutarwa."
Kimanin nau'ukan birrai 600 na macaques suna zaune a cikin gandun daji, suna jujjuyawa daga dogayen bishiyar nutmeg da tsalle akan sanannen haikalin Pura Bukit Sari, kuma ana ɗaukarsu dabbobi masu alfarma.
Gandun dajin da ake karewa a kudu maso gabashin tsibirin Indonesiya ya shahara tsakanin mazauna yankin don hotunan bikin aure, da kuma tsakanin baƙi 'yan yawon bude ido daga kasashe. Kananan birai akan dauke su saman kafada ko cinya don ciyar dasu gyada.
A al'ada, yawon shakatawa shi ne babban tushen samun kuɗi ga mazaunan Bali miliyan 4, waɗanda ke maraba da baƙi sama da miliyan 5 kowace shekara kafin cutar Korona.