Kafofin watsa labarai na Yukren sun yaba Turkiyya saboda cikakkun matakan Covid-19 da ta dauka wajen tabattar da hutu cikin kwanciyar hankali.
Kamfanin dillancin labarai na Yukren ya tunatar da cewa Turkiyya tana daya daga cikin farkon wuraren yawon bude ido da ta bude kofofinta ga 'yan kasar Yukren.
Labaran sun jadadda cewar Turkiyya ta dauki tsauraran matakan kariya na Covid-19 don tabattar da hutu cikin nutsuwa da kwanciyar hanakali ba tare da wata matsala ba.
Da suka kwatanta irin matakan da Turkiyya ke dauka kan Covid-19 a filayen tashi da saukar jirage da kuma wuraren shakatawa, an bayyana cewar a lokacin hutun hadarin kamuwa da Covid-19 a Yukren ya fi na Turkiyya.