A yankuna 17 a Faransa an sanar da cewa a kasance cikin sihrin kota kwana kan yiwuwar mamakon ruwan sama wanda zai iya haifar da ambaliyar ruwa.
Hukumar Kula da Yanayi ta sanar da a kasance cikin shirin kota kwana a yankuna 17 kuma ta yi gargadi a yankuna 69, inda ta bayyana cewar mamakon ruwan sama da ke da tasiri a duk fadin kasar na iya haifar da ambaliyar ruwa.
An bayar da rahoton cewa ruwan zai iya zuwa tare da iska mai gudun kilomita 100.
Mahukunta sun yi kira ga wadanda ke zaune a yankunan da abin ya shafa da su kasance cikin shirin yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa.
Ruwan Kogin Seine da ke Paris, babban birnin kasar ya karu daga mita 4 da santimita 23 zuwa mita 4 da santimita 32 a yau.
A yankin Rhone da ke gabashin kasar, an rufe wasu hanyoyi saboda ambaliyar ruwa.