Yiwuwar afkuwar Tsunami a Amurka

Yiwuwar afkuwar Tsunami a Amurka

An bayar da gargadin yiwuwar afkuwar Tsunami bayan afkuwar girgizar kasa a yankin arewacin Amurka da ya hada da Alaska.

Cibiyar Kula da Afkuwar Tsunami ta Yankin Pacific ta bayyana cewar sakamakon afkuwar girgizar kasa mai karfin awo 7,4 a Kudancin Alaska da tsibirin Alaska, an yi gargadin yiwuwar afkuwar Tsunami.

An bayar da cikakken bayan kan abun da ya faru a teku Oceanic a shafin yanar gizo na tsunami.gov.

An bayyana cewar an ga yiwuwar afkuwar Tsunami a hanyar teku ta Unimak da ke da nisan kilomita 128 daga mashigar Kennedy ta gabar tekun Alaska.

Sanarwar ta ce, ana ci gaba da gudanar da aiyukan ganin ko Tsunamin zai shafi wasu yankunan Amurka na daban, a sanarwa ta gaba za a bayar da bayanai game da hakan.

Sanarwar ta kuma ce, ana bukatar mutanen da ke rayuwa a gabar tekun Alaska da su tashi su koma wurare masu tudu, ko su hau kan rufin kwanon gine-ginensu, kuma kar su je gabar teku.


News Source:   ()