Yiwa mata masu juna biyu allurar rigakafin korona na bayar da kariya ga jariran da zasu haifa

Yiwa mata masu juna biyu allurar rigakafin korona na bayar da kariya ga jariran da zasu haifa

Bincike ya nuna cewa mata masu juna biyu da aka yiwa allurar rigakafin Korona jaririnsu zai kasance mai garkuwa daga kamuwa da cutar. 

A binciken da aka gudanar a lsraila ne aka gano cewa yiwa mata masu juna biyu allurar rigakafin korona na baiwa jariran da zasu haifa zasu samu garkuwa daga cutar.

Binciken da aka yi ta diban jinin jinjirai 40 daga mahaifan matan da aka yiwa allurar rigakafin korona ya nuna cewa dukkaninsu sun samu garkuwa daga cutar. 

Binciken ya nuna muhimmancin yiwa mata masu ciki allurar rigakafin korona. 

Da farko dai ma'aikatar lafiyar lsraila ba ta amince da yiwa mata masu juna biyu allurar rigakafin korona ba, amma daga bisani sun bayar da umarnin hakan.

 

 


News Source:   ()