Ma'aikatar shari'a ta ƙasar ta tabbatar da cewa shugaba Yoon ya zama shugaban ƙasar Korea ta Kudu mai ci na farko da aka haramtawa fita daga cikinta.
Wani babban jami’i a hukumar kula da shigi da fici ta ƙasar Bae Sang-up, ya ce tabbas an haramtawa shugaba Yoon fita daga ƙasar.
A ranar Asabar da ta gabata ne dai shugaban ya tsallake rijiya da baya, a yunkurin tsige shi da aka yi bayan gabatar da ƙudurin hakan da aka gabatar a majalisar dokokin ƙasar.
Sai dai duk da samun nasarar ci gaba da zama a kujerarsa, amma an fara gudanar da bincike kan shugaba Yoon da makusantansa, cikinsu kuwa har da tsohon ministan tsaron ƙasar Kim Yong-hyun, wanda a yanzu ya ke tsare da kuma tsohon ministan harkokin cikin gida Lee Sang-min.
Haka nan wannan doka ta shafi Janar Park An-su, babban jami'in da ke kula da aiwatar da dokar soji kuma ke shugabantar hukumar leken asiri na na ƙasar Yeo In-hyung.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI