Yawan wadanda suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwar Jamus ya haura 156

Yawan wadanda suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwar Jamus ya haura 156

Adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama mai karfi a jihohin Rhineland-Palatinate, North-Rhine-Westphalia da Bavaria a Jamus sun kai 156.

A cikin bayanin da ‘yan sandan Koblenz suka yi, an bayyana cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a cikin bala’in ambaliyar ya karu zuwa 110 a jihar Rhineland-Palatinate.

A cikin sanarwar, an bayyana cewa mutane 670 sun jikkata kuma adadin wadanda suka rasa rayukansu na iya karuwa fiye da haka.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta jihar North-Rhine-Westphalia ita ma ta raba bayanan cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar a jihar ya karu zuwa 45.

A gefe guda kuma, ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya yi tasiri a kudanci da gabashin kasar ya haifar da ambaliyar ruwa da dare.

An ayyana dokar ta baci saboda ambaliyar da zaftarewar kasa a yankin Berchtesgadener Land na jihar Bavaria, wanda ke kan iyakar Austriya.

A cikin bayanin da hukumar yankin tayi, an bayyana cewa akalla mutum daya ya mutu a wannan yankin.

Da haka, yawan mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwa da ambaliyar ruwa a ƙasar ya ƙaru zuwa 156.

A yankin Saechsische Schweiz na jihar Saxony da ke gabashin kasar, an bayyana cewa an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya, koguna sun yi ambaliya, ginshiki na gidaje da tituna sun nutse cika ruwa.


News Source:   ()