Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a bala'in ambaliyar ruwa da ta afku a lardin Nuristan da ke kan iyakar Pakistan a gabashin Afghanistan ya kai 60.
Gwamnan Nuristan Hafiz Abdul Kayyum, a cikin wata sanarwa ga manema labarai, ya tunatar da cewa an samu bala'in ambaliyar ruwa a gundumar Kamdish na Nuristan a ranar 29 ga watan Yuli bayan ruwan sama mai karfi.
Kayyum ya bayyana cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ya karu zuwa 60, kuma har yanzu ana ci gaba da neman sama da mutane 150 da ruwan ambaliyar ya rutsa da su.
Kayyum ya bayyana cewa ana ci gaba da bincike da ceto.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Afghanistan ta sanar da cewa gidaje 150 da gadoji 2 sun lalace sakamakon ambaliyar ruwa.
A cikin sanarwar, an ba da rahoton cewa ba za a iya kai agaji ga wadanda ambaliyar ta shafa ba saboda yankin yana karkashin ikon 'yan Taliban.
Sai dai Taliban ta yi ikirarin wadanda keda bukatar kai gudunmowa a yankin da ibtila'in ruwan ya afkawa zasu iya yin hakan cikin sauki ba tare da wata matsala ba.