Yawan wadanda Korona ta kashe ya fi abinda aka bayyana sau uku a doron kasa

Yawan wadanda Korona ta kashe ya fi abinda aka bayyana sau uku a doron kasa

Samira Asma, wata babbar masaniyar kimiyya a WHO, ta shaida wa manema labarai a wani taron manema labarai cewa idan aka yi la’akari da abubuwan da suka gabata a shekarar 2020, mai yiwuwa yawan wadanda suka mutu daga Korona ya ninka sau biyu zuwa uku.

"Muna sane da cewa an bayar da rahoton mutuwar mutane miliyan 3.4 a hukumance har zuwa wannan watan," kamar yadda ta bayyana yayin da take amsa tambayoyiun daga kanfanin dfillancin labaran Anadolu.

"Abin da muka duba shi ne mutuwar da ta faru ba ta dalilin COVID ba, sannan kuma wadanda aka bayar da rahoto a hukumance, sannan muka kirga yawan karin mace-macen, wadanda suka kai miliyan 3 a shekarar 2020 kawai"

Ta ce cutar ta COVID-19 har yanzu ta na da tasiri kuma WHO na sa ido sosai kan mace-mace a Latin Amurka da Asiya, musamman ma a Indiya da Nepal.

"Don haka ina ganin cewa, kimanin mutum miliyan 6 zuwa 8 na iya zama yawan wadanda cutar Korona ta yi ajalinsu a doron kasa maimakon miliyan 3.4 da aka bayyana a hukumance"


News Source:   ()