Yawan wadanda ke kamuwa da Korona sun karu a Amurka

Yawan wadanda ke kamuwa da Korona sun karu a Amurka

Adadin wadanda ke kamuwa da  coronavirus (Kovid-19) a  Amurka ya wuce dubu 100 a kowace rana a karon farko tun watan Fabrairu.

Lokacin da wannan adadi ya haura sama da dubu 100 lokacin da babu allurar rigakafi a bazara da ta gabata, jami'an kiwon lafiya sun yi korafi akan rashin wadataccen rigakafin.

Rochelle Walensky, darektan Cibiyar Kula da Cututtuka ta (CDC) ta ce "Lokacin da muka kalli asibitocinmu da mace-mace a kasarmu, muna ganin mutane da yawa da ba a yi musu riga -kafi ba."

Kusan rabin asibitocin da aka kwantar da marasa lafiya a makon da ya gabata suna cikin jihohi bakwai na kudancin kasar.

Wadannan jihohin sune Florida, Texas, Missouri, Arkansas, Louisiana, Alabama da Mississippi.

Ma'aikacin jinya na jihar Mississippi Thomas Dobbs ya bayyana cewa,

"Muna ganin karuwar abin mamaki a cikin rahotannin yau da kullun, kuma hakan ya faru ne saboda karuwar kamuwa nau'in Korona ta Delta wacce ta lalata Mississippi kamar tsunami." 


News Source:   ()