Kasar Malesiya ta ba da rahoton samun karin sabbin wadanda suka kamu da Korona har dubu 15,573, wanda shi ne mafi yawa da aka taba samu a rana daya tun daga cutar ta bulla.
Darakta-Janar na Kiwon Lafiya Tan Sri Dokta Noor Hisham Abdullah ya ce sabbin wadanda ke kamuwa da cutar ya karu a fadin kasar zuwa 980,491.
A Selangor ne aka samu mafi yawan wadanda suka kamu da cutar da karin 7,672, sai Kuala Lumpur da ke da 2,063.
A halin yanzu, yawan adadin allurar rigakafin COVID-19 da aka yi ya kai sama da 500,000 a matakin farko.
Ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Adham Baba ya bayyana lamarin a matsayar "Kyakkyawar nasara ce. ga malaman lafiya da sauaran wadanda ke taimakawa wajen yaki da cutar a fadin kasar"