Adadin alluran rigakafin COVID-19 da aka yi a fadin duniya ya haura biliyan 4.36 kamar yadda cibiyar binciken "Our World In Data" wacce ke boibiyar kafar yanar gozon Jami'ar Oxford ta bayyana.
Bayanan da ke akwai akan shafin yanar gizon sun nuna cewa China, inda coronavirus ya fara fitowa a karshen shekarar 2019, ita ce ke jagorantar kididdigar yawan wadanda aka yiwa allurar daga cikin kasashe da yin fiye da biliyan 1.74.
Indiya ta zo ta biyu tare da fiye da miliyan 495, yayin da Amurka ke biye da kusan miliyan 349. Brazil ta gudanar da sama da miliyan 147.
Japan, Jamus, Birtaniya da Faransa suna bin juna yayin da suka ba da sama da miliyan 99.6, miliyan 93.7, miliyan 85.8, da miliyan 75.8, bi da bi.