Jami’an lafiyar yankin na Gaza sun fitar da sabbin alƙaluman ne a jiya Litinin, inda suka ce yara ƙanana aƙalla dubu 17 ne ke cikin jimillar mutanen sama da dubu 45 da rayukansu suka salwanta a tsawon watanni 14 da aka shafe Isra’ila na yaƙar Hamas a zirin na Gaza.
Zalika akwai kuma wasu yaran Falasɗinawa na dabam aƙalla dubu 11,000 da suka ɓace, waɗanda ake kyautata zaton ɓaraguzan gini ne suka danne su, har zuwa wannan lokaci kuma ba a gano su ba. Adadin waɗanda suka jikkata kuwa a yanzu ya kai mutane aƙalla dubu 106,962.
Ma’aikatar lafiyar yankin na Gaza ta ƙara da gargaɗin cewa hare-hare babu ƙaƙƙautawa da Isra’ila ke cigaba da kaiwa a sassan zirin ya jefa Falasɗinawa kusan miliyan guda cikin mummunar haɗarin tagayyara baya ga tashin hankalin da suke ciki, la’akari da cewar yanayin tsananin sanyi na gaf da riskarsu.
Alƙaluman dai sun nuna cewar yawan mutanen da Isra’ila ta halaka a Gaza ya kai aƙalla kashi 2 na jimillar Falasɗinawa kimanin miliyan biyu da dubu 300 dake rayuwa a Zirin gabanin ɓarkewar yaƙin da hare-haren Hamas kan Isra’ila na ranar 7 ga watan Oktoban shekarar bara suka janyo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI