Adadin mutanen da suke "jin kaɗaici" a Tarayyar Turai (EU) ya ninka saboda sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19).
Dangane da rahoto kan "kadaici da keɓancewar jama'a" wanda Cibiyar Nazarin Hadin Gwiwa ta Kungiyar EU ta wallafa, yayin da kashi 12 cikin ɗari na 'yan ƙasa na EU suka ji kaɗaici, damuwa ko rashin jin daɗi a cikin shekarar 2016, wannan adadin ya karu zuwa kashi 25 cikin ɗari a farkon watannin annobar Covid-19.
Waɗanda ke zaune su kaɗai sun fi fuskantar bakin ciki da kashi 22 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2016, yayin da waɗanda ke zaune tare da abokai ko yara ya karu da kashi 9 cikin ɗari.
‘Yan shekaru 18 zuwa 25 sun fi fuskantar tasiri game da dokokin nisantar juna. A ‘yan wannan shekarun, saurin jin kadaici ya karu sau 4.
Kafin annobar, jin kadaici ya kai kusan kashi 6 a Arewacin Turai da kashi 11 zuwa 13 a sauran yankuna ukun. Tare da annobar, adadin ya karu zuwa kashi 22 zuwa 26 tare da bambancin a yankuna.
Adadin jin kadaici na maza da mata dake zama a birni ko ƙauye ya kasance iri daya ba tare da wani bambanci ba.
Yanayin tattalin arziki mai kyau da kyakkyawan yanayin kiwon lafiya sun kare mutane daga kadaici kafin annobar da kuma bayanta.
Labaran da aka wallafa kan batun kadaici da ‘yan jaridu a Tarayyar Turai suka yi sun ninka sau biyu a lokacin annobar, kuma an samu sauyi a fadakarwa kan batun a kasashen kungiyar EU.