Yawan marasa gidaje zai karu a Amurka

Yawan marasa gidaje zai karu a Amurka

Wani farfesa a jami’ar Columbia ya bayyana cewar kasancewar yadda Covid-19 ke ruguza tattalin arziki dake haifar da rashin aikin yi yawan marasa gidaje a Amurka zai karo da kaso 45 cikin dari.

Haka na nufin karin wasu dubu 250,000 ko fiye da haka a cikin yawan wadanda basu da gidaje dubu 568,000 a alkaluman Janairun 2019.

Jihar California ce zata kasance mai karancin karin yawan wadanda basu da matsugunan daga kimanin dubu 150,000 zuwa 180,000 watau karin kaso 20 cikin dari idan aka kwatanta da sauran jahohin kasar.

Binciken ya ta’laka ne akan karin yawan marasa aikin yi a kasar inda aka bayyana cewar sauran kananan jahohi zasu samu karin marasa gidaje da yawa fiye da Calfornia inda kimanin kaso daya bisa hudun marasa gidaje a kasar suke.


News Source:   www.trt.net.tr