Yawan asarar da aka tafka a Gaza cikin watanni 15 na yaƙin Isra'ila a yankin

Yawan asarar da aka tafka a Gaza cikin watanni 15 na yaƙin Isra'ila a yankin

Wannan adadi ya ƙunshi iyalai dubu 1 da 600 waɗanda aka kawar da su baki ɗaya ya zama basu da sauran zurriya a ban ƙasa.

Sai kuma ƙananan yara dubu 17 da 841 da Isra’ilan ta kashe, biye da wasu yaran 44 da tsananin yunwa ya yi ajalinsu saboda yadda Isra’ila ta hana shigar da abinci da ruwan sha yankin mai fama da ƙawanyar tsawon shekaru.

Akwai kuma wasu yaran na daban 8 wadanda suka mutu sanadiyyar tsananin sanyi a asibitoci bayan da Isra’ilar ta katse lantarkin yankin.

A gefe guda alƙaluman da Aljazeera ta tattara ya nuna yadda Isra’ila ta hallaka jami’an kiwon lafiya a yankin na Gaza waɗanda yawansu ya kai dubu 1 da 68 baya ga ƴan jarida 202 adadi mafi yawa da aka kashe a wani yaƙi.

Haka zalika alƙaluman sun nuna yadda yara dubu 35 da 74 suka rasa dukkanin ɓangarorin iyayensu a hare-haren na Isra’ila wanda ya kashe ilahirin iyayensu mata da maza a watannin 15.

Akwai rukunin gidaje dubu 161 da 600 waɗanda Isra’ilar ta rushe baki ɗaya sai kuma asibitoci 34 da suma ta lalata su.

Wasu bayanai sun nuna cewa galibin makarantun yankin na Falasɗinu sun zama kufai lura da cewa Isra’ila ta yi ta ƙaddamar da hare-hare kansu ba ƙaƙƙautawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)