Hukumar wadda ta kafa hujja ta alƙaluman ma’aikatar lafiya ta Gaza, ta ce baya ga ɗimbin mutanen da Isra’ilan ta kashe waɗanda aka tattara alƙalumansu zuwa fiye da mutum dubu 55, akwai kuma wasu aƙalla dubu 11 da suka ɓace wasunsu suna tsare a hannu mahukuntan na Isra’ila wasu kuma an kashe su ba tare da sanin gawarwakinsu suke ba.
Ƙarƙashin dokokin da Isra'ila ta gindayawa al'ummar yankin na Falasɗinu dukkanin waɗanda suka fita ko dai da sunan hijira ko kuma tserewa hare-haren ƙasar ta Yahudu kai tsaye basu da ƴancin sake dawowa ci gaba da rayuwa a cikin yankin mai fuskantar mamaya.
Zuwa yanzu fiye da mutum dubu 108 Isra'ilan ta jikkata a hare-harenta, galibinsu waɗanda ta yanke musu wasu sassa na jikinsu kama daga ƙafa zuwa hannu.
Ko a safiyar yau Alhamis Isra'ilan ta kashe fiye da mutane 28 ciki har da wasu mutum 11 a tudun mun tsira na al-Mawasi, a dai dai lokacin da ake ganin tsanantar ambaliyar ruwa a zirin na Gaza sakamakon mamakon ruwan sama ba ƙaƙƙautawa.
A gefe guda ɗimbin jarirai sabbin haihuwa ne ke ci gaba da mutuwa a asibitocin na Gaza sakamakon katse lantarki da kuma tsananin sanyin da ake fuskanta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI