Duk da cewar wasan za’a ayyana buɗe shi a jibi Juma’a 26, ga watan Yulin da muke ciki a hukumance, hakan ba zai hana karsashin magoya baya da 'yan kallo ba , wajen cigaba da kallon wasanni masu ƙayatarwa biyo bayan fara wasannin.
A yau Laraba ne ake sa ran fara gudanar da wasan ƙwallon ƙafa da ƙwallon zari Ruga ta ƴan wasa 7 wato Rugby 7, Inda tuni ƴan wasa da ƙungiyoyin su, sun gama hallara tun a jiya.
A matsayin sharar fage za’a gudanar da wasan zari-ruga ta ƴan wasa 7, a yau ɗin, tsakanin tawagun ƙasashen da suka halarci gasar ta bana, kuma za a fara ne tun da misalin ƙarfe 3:30 na yammaci har zuwa ƙarfe 10 na daren yau, kuma duk wasannin za su gudana ne a filin wasa na Stede De France, kazalika a gobe Alhamis sauran tawagun za su fara fafata wa, tun da misalin ƙarfe 2 na rana har zuwa ƙarfe 5 na yamma a zagayen farko, yayin da a zagaye na biyu kuma wasu jerin tawagun za su fafata tun da misalin ƙarfe 8 na dare har zuwa ƙarfe 11 na dare.
Ana sanya rana gasar zata karbi bakuncin shugabannin kasashe sama da 100 REUTERS - Kai PfaffenbachA jibi Juma’a ne dai, za’a gudanar da bikin buɗe gasar inda ake sa ran mutane dubu ɗari 5 za su halarci kogin Sins da ya ratsa ta tsakiyar birnin Paris, kuma ƙasashe sama 200 ne za su halarci wasannin.
Filayen da za a gudanar da ɗaukacin wasannin sun haɗar da Bercy arena, da porte de la chapelle arena da Paris La Defense arena, sai Aquatics centre da Stede de France da North Paris Arena da kuma Le Bourget sport climbing venue.
Sauran sun haɗa da Saint Quentin-en-Yvelines da Elancourt Hill da Le golf National da Saint Quentin-en-Yvelines Velodrome sai kuma Chateau de Versailes.
A wasannin na yau akwai ƙasashen Afrka guda 3 da zasu fafata a kwallon ƙafa 3 inda ake fatan zasu bi sahnun Najeriya da Ghana wajen lashe lambobin zinare.
Tuni manyan mawaka na duniya suka fara hallara a birnin na Paris don nishadantar da mahalarta taron via REUTERS - CHRISTOPHE PETIT TESSON
Bayanai sun ce an aike da jami’an tsaro sama da dubu ɗaya don bayar da tsaron a filin wasan da za’a kara tsakanin Mali da Isra’ila don tabbatar da tsaro yadda ya dace, kasancewar sa ɗaya daga cikin wasanni mafiya ɗaukar hankali a yau.
Wannan shine karo na farko da Faransa ke ɗaukar nauyin gasar cikin shekaru 100 da suka gabata, lamarin da ke ƙarawa gasar armashi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI