Yau za a fara Sallar Juma'a a Hagia Sophia

A ranar Juma'ar nan za a Sallar Juma'a a Hagia Sophia bayan shekaru 86 da dakatar da hakan

Hukumar Kula da Al'amuran Addinai ta Turkiyya Diyanet ta gara shirin bude Hagia Sophia da karanta Addu'o'i. Za a gudanar da karatun Alku'rani sanna shirin zai kawo karshe tare da Addu'a daga bakin Shugaban Diyanet Ali Erbas.

Tun da Asubah 'yan kasa da ke son yin Sallar Juma'a ta farko a Hagia Sophia suka taru a gaban Masallacin.

Saboda annobar corona, ma'aikata a wajen na ba wa mutane abun wanke hannu, dardumar Sallah da kuma gwada zafin jikinsu

An ga 'yan yawon bude ido na gida da na waje a wajen da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da shugaban jam'iyyar MHP Devlet Bahceli zansu jagoramci budewa.

An dauki tsauraran matakan tsaro a wajen.


News Source:   ()