Yau talata Amurkawa ke zaben sabon shugaban ƙasa da zai gaji Joe Biden

Yau talata Amurkawa ke zaben sabon shugaban ƙasa da zai gaji Joe Biden

Amurkawan za su kaɗa ƙuri’unsu yayin da tuni masu yin zabe da wuri kusan miliyan 80 suka jefa ƙuri’unsu ta akwatin gidan waya ko kuma ta hanyar kaɗa ƙuri’ar wuri a ƙasar.

Zaben da za’a fafata tsakanin ƴan takara musamman Kamala Harris da Donald Trump, shine zai rarrabe wurin sanin wanda zai maye gurbin shugaba mai ci Joe Biden bayan kammala wa’adinshi.

Tsohon shugaban ƙasar Amurka Donald Trump na jam’iyyar Republican shine zai kara da Kamala Harris a zaben na yau, kuma ana ganin zaben wata dama ce gareshi na sake komawa mulkin Amurka bayan rashin nasara da ya yi a zaben shekarar 2020 inda ya sha kaye a hannun shugaba Joe Biden.

Kamala Harris dai ita ce mace baƙar fata ta farko da ta zama mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka bayan kada Trump da suka yi takara da shugaba Biden a jam’iyyar Democrate.

Ana ganin wannan zabe a matsayin babbar dama ga Kamala Harris ta kafa tarihin zama mace ta farko kuma baƙar fata da za ta zama shugabar ƙasa a Amurka.

Zaben na bana ya zo ayyin da rikice-rikice suka mamaye gabas ta tsakiya , wani abu da ake hasashen ka iya yin tasiri wurin zaben na yau.

Tuni hankalin duniya ya karkata kan zaben mai cike da jan hankali tsakanin manyan ƴan takara Kamala Harris da Donald Trump

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)