A shekarar 1948 Majalisar Ɗinkin Duniya ta jagoranci ƙasashe wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar mutunta ‘yancin ɗan Adam ba tare da yin la’akari da ƙasa, ƙabila, jinsi ko kuma addini ba.
Kundin wannan yarjejeniya ta kare hakkin ɗan Adam na daga cikin kundayen dokokin ƙasa da ƙasa masu matuƙar muhimmanci a tarihin duniya, wanda aka samar da shi bayan masifun da aka gani na mutsuttsuke ‘yancin ɗan Adam yayin da ake gwabza yaƙin duniya na biyu, lamarin da ya sa shugabannin ƙasashe cimma matsayar gaggauta samar da dokokin baiwa mutane kariya daga zalunci, da cin zarafi da kuma nuna wariya.
Ranar kare hakkin ɗan Adam ɗin ta bana da aka yi wa taken ‘Yancinmu, Gobenmu, A Yanzu’, ta zo ne a daidai lokacin da laifukan tauye ‘yancin na bil Adaman suka zama ruwan dare a sassan duniya, sakamakon yawaitar yaƙe-yaƙe, da sauran tashe-tashen hankula, baya ga sauran nau’ikan cin zarafin da ɗaiɗaikun mugaye riƙaƙƙu ke aikatawa.
Sai dai a iya cewa an samu cigaba ta wani fannin, duba da cewar cikin gwamman shekarun da suka gabata, ƙasashe da dama sun samar tare da aiwatar da dokoki makamantan na Majalisar Ɗinkin Duniya, domin tabbatar da daidaiton jinsi, haramta bauta, da kuma bai wa tsirarun kabilu kariya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI