Yau Amurkawa ke kaɗa kuri'a domin zaɓen sabon shugaban ƙasa

Yau Amurkawa ke kaɗa kuri'a domin zaɓen sabon shugaban ƙasa

An bude rumfunan zaɓe a faɗin Amurka, bayan da ƴan takarar biyu tsohon shugaban kasar Donald Trump na jam’iyyar Republican da mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris dake yi wa jam'iyyar Democrat mai mulki takara suka shafe watanni suna fuskantar juna tare da shimfida alkawuran yaƙin neman zaɓensu kan batutuwan da suka shafi kiwon lafiya da shige da fice da tattalin arziki.

Ƙuri'un gidan waya

Tuni Amurkawa sama da miliyan 78 suka kada kuri'a da wuri ta hanyar aika wasiku ko kuma da kansu kafin ranar ta yau.

A ranar ƙarshe ta yakin neman zabe, Trump ya gudanar da jerin gwano a jahohin da ke da matukar muhimmanci, wanda ya fara daga North Carolina kafin ya nufi Pennsylvania don inda ya ƙarƙare yakin neman zabe Michigan

Ɗan takarar Republican a zaben Amurka Donald Trump Ɗan takarar Republican a zaben Amurka Donald Trump © 路透社图片 Harris tana kammala kamfen ɗinta a Pennsylvania ta hanyar gudanar da tarurruka a Philadelphia da Pittsburgh.

Ana sa ran Donald Trump zai kalli yadda sakamakon ke fitowa daga gidansa na Mar-a-Lago a Palm Beach, dake Florida, yayin da anata bangare Kamala Harris zata zaman bibiyar al’amura a Jami'ar Howard dake Washington DC.

Mataimakiyar shugaban Amurka, kuma ƴar takarar neman shugabancin Amurka Kamala Haris Mataimakiyar shugaban Amurka, kuma ƴar takarar neman shugabancin Amurka Kamala Haris REUTERS - JONATHAN ERNST

Kamala Harris dai ita ce mace baƙar fata ta farko da ta zama mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka bayan kada Trump da suka yi takara da shugaba Biden a jam’iyyar Democrate.

Ana ganin wannan zaɓe a matsayin babbar dama ga Kamala Harris ta kafa tarihin zama mace ta farko kuma baƙar fata da za ta zama shugabar ƙasa a Amurka.

Zaben na bana ya zo ayyin da rikice-rikice suka mamaye gabas ta tsakiya , wani abu da ake hasashen ka iya yin tasiri wurin zaben na yau.

Tuni hankalin duniya ya karkata kan zaɓen mai cike da jan hankali tsakanin manyan ƴan takara Kamala Harris da Donald Trump

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)