Ibtila’in da ya faro a ranar 26 ga watan Disamban 2004 anga tumbatsar tekun India da ya shafi dukkanin biranen da ke gaɓa da shi tun daga Indonesia har zuwa Somalia lamarin da ya yi gagarumar illa marar misaltuwa ga al’ummomin wannan yankuna baya ga barin tabon da masana ke ganin zai yi tarin duniya ya manta da shi.
Ibtila'in shi ne mafi muni da Duniya ta gani a tarihi. AP - KARIM KHAMZINIbtila’in wanda aka bayyana da mafi muni da duniya ta gani ya shafi yankunan ƙasashe 14 da guguwar ta tsunami haɗe da girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 9.1 da kuma zaftarewar laka baya ga tumbatsar teku suka shafa.
Domin bikin tunawa da wannan rana mafi muni ne kuma dandazo mutane a ƙasashe da dama na nahiyar Asia suka gudanar da wani taron jimamin wannan ibtila’i na Tsunami da ya hallaka mutane fiye da dubu 220, da kaso mai yawa a Indonesia inda mutane fiye da dubu 100 suka mutu a rana guda, lamarin da ya tilasta fara buga amsa kuwwar ankararwa a babban masallacin ƙasar na Baiturrahman don sanar da mutane shiga cikin shirin ko ta kwana hatta a ƙasashen Sri Lanka da India da kuma Thailand waɗanda annobar ta isa garesu sa’o’i bayan afkuwarta a Indonesia.
Taron addu'ar tunawa da ibtila'in na Tsunami a Indonesia, ƙasar da ibtila'in ya fi yiwa illa fiye da ko'ina. AP - Reza SaifullahYayin gangamin tunawa da wannan ibtila’i iyalai sun kai ziyara ga manya-manyan ƙaburburan da aka birne tarin mutanen da ka yi musu jana’izar bai ɗaya tare da birne su a waje guda don yi musu addu’o’i.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI