Yau ake cika shekara ɗaya da kai harin da mayaƙan Hamas suka yi cikin Isra'ila

Yau ake cika shekara ɗaya da kai harin da mayaƙan Hamas suka yi cikin Isra'ila

Tun bayan kai wancan hari da mayaƙan Hamas suka yi a ranar 7 ga watan Oktoban bara, a ranar 8 ga watan ne kuma Isra’ila ta ƙaddamar da harin ramuwar gayya kan Falasdinawa.

Wasu alkaluma da ma’aikatar kula da lafiyar Gaza ta fitar, sun nuna cewa sama da Falasɗinawa dubu 42 yawancinsu mata da ƙananan yara ne Isra’ila ta kashe.

Manyan ƙasashe masu faɗa aji a duniya sun yi ƙoƙarin warware wannan rikici da ayanzu ya bazu a yankin Gabas ta Tsakiya amma abin yaci tura, lamarin da ya sanya dubban mutane fitowa zanga-zangar nuna rashin jin daɗi game da asarar rayukan da ake samu.

Yadda aka gudanar da zanga-zanga a birnin Rabat na Morocco a jiya 6 ga watan Oktoban shekarar 2024. Yadda aka gudanar da zanga-zanga a birnin Rabat na Morocco a jiya 6 ga watan Oktoban shekarar 2024. © AFP

Ko a ƙarshen makon nan daya gabata, sai da aka gudanar da zanga-zanga a manyan birane irinsu Washigton da New York da Landon da Sydney da Jakarta da Istanbul da Rabat da dai sauransu.

Masu zanga-zangar dai, na buƙatar Amurka ta dakatar da baiwa Isra’ila makaman da ta ke yi da sunan kare kanta, sannan kuma ta dakatar da hare-haren da tafa kaiwa Lebanon a yakin da ta ce tana yi da mayakan Hezbollah.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. REUTERS - Eduardo Munoz

Shi dai Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce ba komai ya sanya su daukar wannan mataki ba, sai don kare sake faruwar harin 7 ga watan Oktoban bara da Hamas ta kai musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)