Wani rahoto da hukumar ƴaki da cutar kanjamau ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, ya ce aƙalla mutane miliyan ɗaya da dubu ɗari uku ne suka kamu da cutar a shekarar 2023 da ta gabata.
Wannan ya nuna cewa ansamu ninkin adadin da ake bukata har sau uku kafin cimma buƙatar majalisar ɗinkin duniya na kawar da cutar mai barazana ga lafiyar al’umma a shekarar 2030.
Kusan mutane 630,000 ne suka rasu rayukansu sakamakon cutar ƙanjamau a shekarar da ta gabata, adadi mafi ƙanƙanta tun bayan rashin da aka yi na mutane miliyan 2.1 a shekarar 2004.
Ansamu gagarumar nasara a yaƙi da cutar wajen amfani da magunguna da allurori da ke rage yawan ƙwayoyin cutar da mutum ke ɗauke da shi.
Rahoton ya ƙara da cewa, cikin mutane miliyan 40 da ke fama da cutar a faɗin duniya, wasu kusan miliyan 9.3 ba sa samun kulawar likitoci, kuma duk da tarin nasarorin da ake samu, sai da aka samu rahoton ƙarin masu fama da cutar a wasu ƙasashe 28.
Mataimakin shugaban hukumar yaƙi da cutar ƙanjamau na Majalisar Ɗinkin Duniya, Christine Stegling ta ce ansamu nasarori da dama ta hanyar amfani da magunguna da allurori, da kuma tabbatar da haƙƙin ɗan Adam, da ayyukan jin ƙai.
Sai dai ta ce har yanzu akwai sauran runa-a-kaba wajen tabbatar da haƙƙin ɗan Adam,wanda ke barazana ga ƙoƙarin kawo cutar ƙanjamau a faɗin Duniya, inda ta yi gargaɗin cewa idan har aka ci gaba da tafiya a haka, to tabbas baza’a iya cimma burin kawo ƙarshen cutar ba nan da shekarar 2030.
Me yake janyo cutar ƙanjamau?
Akwai hanyoyi da dama da ake samun cutar ƙanjamau, sai dai waɗanda aka fi samu ta hanyarsu shi ne wajen yin mu’amula tsakanin mace da namiji, wanda ita ce silar samun kyasa-kyasai da dama na masu ɗauke da cutar..
Sai kuma ta hanyar taɓa jinin wanda ke ɗauke da cutar, misali; idan aka yi amfani da sirinjin allurar da aka yiwa mai ƙanjamau, wajen yi maka allura, sai kuma ta hanyar haihuwa, ko shayarwa.
Shin mene Alamomin da ke nuna cewa mutum ya kamu da cutar ƙanjamau?
Alamomi da ke nuna cewa mutum ya kamu da cutar ƙanjamau sun haɗa da zazzabi, ciwon kai mai zafi, ciwon jiki, ciwon maƙogaro, amai da gudawa, rama da dai sauransu.
Abubuwan da masu cutar ƙanjamau ke fuskanta a cikin al’umma.
Wasu daga cikin abubuwan da ke addamar masu cutar ƙanjamau su ne wariya da ƙyama, rashin samun kulawa ta musamman daga ƴan uwa, yanayin tattalin arziƙi da ke hana masu fama da cutar samun damar amfani da magungunan da suka dace domin yaƙar cutar.
Mene ne hanyoyin magance cutar?
Babu wata hanya guda ɗaya tilo da ake bi wajen magance cutar ƙanjamau ko wani magani, sai dai a kan yi amfani da magunguna domin taƙaita zafafar cutar a jikin mutum, kana magungunan sun rage yawaitar mace-mace da ake samu sanadiyyar cutar a faɗin duniya.
Taken bikin na bana dai shi ne “abi hanyoyin da suka dace”, yin duba kan abubuwan da ke damun masu fama da cutar, tare da tallafa musu domin gobensu ta yi kyau.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI