Yau aka cika shekaru 3 cif da faro yaƙin Rasha da Ukraine

Yau aka cika shekaru 3 cif da faro yaƙin Rasha da Ukraine

A jawabinsa ga al’ummar Ukraine, shugaba Volodymyr Zelensky a yau Litinin ya yabawa jama’ar ƙasar waɗanda ya kira da jajirtattu masu kishin ƙasa lura da shekaru 3 da suka shafe suna tirjiya ga mamayar Rasha.

Taron cika shekaru 3 da faro yaƙin na zuwa a dai dai lokacin da shugabar hukumar gudanarwar EU Ursula von der Leyen da Firaministan Canada Justin Trudeau da sauran manyan jami’an ƙungiyar EU ke ziyara a ƙasar ta gabashin Turai.

Wannan taro dai ya gudana ne ba tare da wakilcin ko mutum guda daga Washington ba, lamarin da ke nuna halin ko in kula da Donald Trump ke nunawa wannan ƙasa wadda ta samu cikakken goyon bayan Amurka ƙarƙashin mulkin Joe Biden.

Cikin jawabin Zelensky, ya yi godiya da jinjina ga dukkanin ɓangarorin da ya ce da taimakonsu Ukraine ta ci gaba da tsaywa da ƙafafunta, musamman al’ummar ƙasar da ya miƙa musu godiya ta musamman kan jajircewarsu.

A gefe guda, Ursula ta sake nanata alwashin EU na taimakawa Ukraine a dukkanin matakai don ganin ƙasar ta kai ga nasara.

Taron na zuwa gabanin haɗuwar da shugabannin EU ke shirin yi a ranar 6 ga watan Maris mai kamawa don tattaunawa kan yadda za su ci gaba da tallafawa ƙasar bayan janyewar Amurka.

Bugu da ƙari ƙasashen na EU sun kuma amince da ƙarin takunkumai har 16 ga Rasha kodayake jagoran Hungary Viktor Orban kuma aboki ga Putin ya ce sam ƙasar shi ba zata goyi bayan takunkuman ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)