Yarjejeniyar tsaro tsakanin kasashen Girka da Isra’ila

Yarjejeniyar tsaro tsakanin kasashen Girka da Isra’ila

Ma’aikatar Tsaron Isra’ila ta sanar da cewa Girka ta amince da yarjejeniyar tsaro ta dala biliyan 1.68 na shekaru 20 da Isra’ila.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaron ta fitar, an bayyana cewar Gwamnatin Athens ta amince da yarjejeniyar tsaro wacce ta kunshi siyan jirgin horaswa daga Isra’ila kuma amicewa da wani kamfanin Isra’ila don kafa makarantar koyar da tukin jirgin sama a Girka.

A karkashin yarjejeniyar, kamfanin masana'antar tsaro ta Isra'ila, Elbit Systems zai kafa kuma ya gudanar da aiyukan makarantar tukin jirgin sama ta rundunar sojojin sama ta Girka.

Yarjejeniyar tsaron ta kuma kunshi abubuwa kamar sayar da jirgin horaswa 10 M-346 da Isra’ila ta yi ga Girka, kula da jirgin saman T-6 Efroni da tallafi ga tsarin simulator na kamfanin Elbit Systems.

An bayyana cewar yarjejeniyar ta shekaru 20 da Girka ta amince da ita ce yarjejeniyar samar da tsaro mafi girma tsakanin kasashen biyu har zuwa yau.


News Source:   ()